1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kama jagoran 'yan adawa na Zimbabuwe

Suleiman Babayo LMJ
June 17, 2024

An kama jiga-jigan 'yan adawa na Zimbabuwe inda aka tuhume su da zargin neman tayar da hankali sakamakon haduwa da suka shirya a karshen mako..

'Yan sandan Zimbabuwe
'Yan sandan ZimbabuweHoto: Luis Tato/AFP via Getty Images

'Yan sanda a kasar Zimbabuwe sun kama jarogan 'yan adawa Jameson Timba  da magoya bayansa fiye da 70 da ake tuhuma  da neman tayar da hargitsi sakamakon wata haduwa da suka yi a karshen mako.

Shi dai Timba yake jagorancin gangamin 'yan adawa na Citizens Coalition for Change (CCC) tun lokacin da tsohon jagoran 'yan adawa Nelson Chamisa ya ajiye aiki a watan Janairu da ya gabata. Mutanen da aka kama suna ofisoshin 'yan sanda biyu da ke birnin Harare fadar gwamnatin kasar. Ita dai Zimbabuwe da ke yankin kudancin Afirka tana cikin kasashen da suke sahun gaba inda ake nuna tsangwama ga 'yan adawa.

A shekarar da ta gabata Shugaba Emmerson Mnangagwa mai shekaru 81 ya sake lashen zaben shugaban kasa da kashi 52.6 cikin 1000 yayin da jagoran adawa na lokacin Nelson Chamisa ya samu kashi 44 cikin 100.