1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai samame mabuyar 'yan Ipob

Ramatu Garba Baba
April 23, 2022

Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kama wasu 'yan rajin Biafra na Kungiyar IPOB da aka jima ana nema bisa laifin hannu a tashe-tashen hankula a yankin Kudancin kasar. 

Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Wani mai magana da yawun rundunar reshen jahar Imo, Michael Abattam, ya sheda ma manema labarai cewa, an kai samame mabuyarsu a ranar Larabar da ta gabata bayan da aka kwarmata masu bincike mabuyar da suka mayar wajen kera bama-baman da suke amfani da su a kai hare-hare a yankin tare kuma da kwace wasu tarin makamai.

Daya daga cikinsu ya taimaka wa bincike wajen amsa laifin kera abubuwan fashewar in ji jami'in. Sai dai a wani martani da kungiyar mai son ballewa daga Najeriyar ta mayar a wannan Asabar, ta nesanta kanta da ma 'yan kungiyar daga batun kera bama-baman da ma hare-haren da gwamnatin Najeriya ta ce, sun yi asarar rayukan mutum sama da dari da talatin daga shekarar da ta gabata.