An kama wata 'yar jarida a Jamhuriyar Nijar
June 11, 2020Talla
Wani da ga na kusa da Shugaba Mahamadou Issoufou ne ya shigar da karar Samira sabou, a cewar kafofin watsa labarai da dama na kasar ta Nijar. Cikin sanarwar da ta wallafa a shafukan sada zumunta na zamani, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce tsare 'yar jarida Samira Sabou ba wani abu ba ne illa kawo tarnaki ga ayyukan kungiyoyin fararen hula da kuma kafafen yada labarai don dakile badakalar makamai.
Mai shari’a ya ba da sanarwa a ranar 8 ga Afrilu cewa a bude bincike kan badakalar makamai da ta barke a watan Fabrairu, bayan da wani binciken da Shugaba Issoufou ya nemi a gudanar ya bayyana adadin kudaden da aka biya wajen sayen makamai a fafatawa da masu jihadi a kudu maso gabas da kuma yammacin kasar.