1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kame jagoran masu zanga-zanga a Maroko

Mohammad Nasiru Awal AH
May 29, 2017

Majiyoyin gwamnati sun ce 'yan sanda sun kame dan gwagwarmayar Nasser Zefzafi mai shekaru 39 da haihuwa.

Marokko Nasser Zefzafi, Anführer Protestbewegung
Nasser Zefzafi dan gwagwarmaya kuma jagoran masu bore a MarokoHoto: Reuters/Y. Boudlal

A kasar Maroko an cafke jagoran zanga-zangar nan da aka kwashe watanni da dama ana yi. Majiyoyin gwamnati sun ce 'yan sanda sun kame Nasser Zefzafi mai shekaru 39 da haihuwa. A ranar Jumma'a da ta gabata mahukunta suka bada sammacin kame dan gwagwarmayar bayan da ya kawo tsaiko lokacin hudubar wani limani a wani masallacin Jumma'a da ke birnin Al-Hoceima, inda kwanaki uku a jere a ranar Lahadi daruruwan mutane suka fantsama kan titunan birnin suna sowa suna zargin yawaitar cin hanci da rashawa a kasar. Zanga-zangar da ta kasance karkashin jagorancin Zefzafi a watannin bayan nan, na da nasaba da rashin aikin yi, da tabarbarewar sha'anin kiwon lafiya da matsalar cin hanci da rashawa a yankin arewacin kasar ta Maroko. Da yammacin ranar Lahadi an yi zanga-zanga a wasu biranen ciki har da Rabat babban birnin kasar.