An kame wani babban kwamnadan Taliban a kudancin Afghanistan
May 19, 2006Rahotanni daga Afghanistan sun ce an kame wani babban kwamandan kungiyar Taliban mai ra´ayin kishin Islama. Kafofin yada labaru sun rawaito rundunar tsaron Afghanistan na cewa dakarun kasa da kasa sun cafke Mullah Dadullah a lardin Kandahar mai fama da rikici. Har yanzu kuwa ´yan sandan kasar na ci-gaba da farautar ´ya´yan kungiyar Taliban bayan mummunar fafatawa da aka yi tsakanin mayakan Taliban din da dakarun gwamnati da na ketare a daya hannun. Shugaba Hamid karzai ya zargi Pakistan da marawa ´yan tawayen dake kudancin kasar baya. Karzai ya ce makarantun Islama dake makwabciyar kasar kan turo ´yan makaranta cikin Afghanistan inda suke bankawa makarantu da asibitoci wuta. Akalla mutane 100 suka kwanta dama sakamakon kazamain fadan da aka gwabza cikin wannan mako.