An kammala babban taron jam´iyar CDU a birnin Düsseldorf
December 7, 2004Babban taron na jam´iyar Christian Democratic Union wato CDU a takaice da ya gudana a birnin Düsseldorf ya tabbatar a fili yadda jam´iyar ke shan wahala wajen sake maido da martabarta musamman na rike madafun iko a cikin kawance da take yi da CSU. An ga haka a shirye-shiryen gudanar da wannan taro da kuma karfin tsayar da kwakkwarar shawara tsakanin ´ya´yanta. Ko da yake a rubuce komai na tafiya daidai wa daida. Alal misali jam´iyar ta cimma tudun dafawa a muhimman batutuwan da suka shafi yiwa tsarin zaman jama´a canje-canje, amma ta kasa kawad da bambamce-bambamce da take fuskanta dangane da manufofin kiwon lafiya. Angela Merkel wadda aka sake zaben ta a mukamin shugabar jam´iyar ta CDU na hankoron zama ´yar takarar shugaban gwamnati shekaru biyu masu zuwa.
Amma idan aka dubi hakan da idanun basira za´a ga cewar har yanzu da akwai abubuwan dake hana ruwa gudu bisa manufa. Alal misali daidaiton da aka cimma akan manufar kiwon lafiya ya matukar damawa kwararrun masana harkokin kiwon lafiya na jam´iyun adawa lissafi tare da harzuka wadanda suka so jam´iyun sun yi gaban kansu. Martabar jam´iyun na Christian Union dai ta zube. Musamman bayan da suka ki bin shawarar da daya daga cikin shugabannin ta wato Friedrich Merz ya bayar dangane da yiwa dokokin haraji canje-canje, duk kuwa da amincewa da wannan shawara da mahalarta wani babban taron jam´iyun suka yi a lokacin baya. Hakan dai ya sa Friedrich Merz ya ajiye mukamin shi a cikin jam´iyun hadin gwiwar.
Hakan kuwa ya kasance babban koma baya ga Angela Merkel da shugaban jam´iyar CSU kuma firimiyan jihar Bavariya Edmond Stoiber wajen nemawa kansu alkiblar da ta dace. Maimakon su mayar da hankali wajen sukar lamirin gwamnati da kuma kokarin hade kawunansu, sai suka shagala wajen yin wasu abubuwa na daban.
Yanzu dai shugabar jam´iyar ta CDU wato Angela Merkel ta fara jinshi a jika, domin ko da yake an sake zaben ta da yawan kuri´u kimanin kashi 90 cikin 100, amma bai kai yawan kuri´un da ta samu shekaru biyu da suka wuce ba. Kamata yayi nan gaba dukkan shugabanni da masu fada a ji cikin jam´iyar su zama tamkar tsintsiya madaurinki daya, kamar yadda ra´ayin mahalarta taron na birnin Düsseldorf ya nunar.