1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala musayar fursunoni a Yemen

April 16, 2023

Bangarorin da ke gaba da juna a Yemen sun kammala musayar fursunoni da suka fara a 'yan kawanakin nan, fursunonin da ke da alaka da yakin da kasar ta fada yau tsawon shekaru.

Hoto: KHALED ABDULLAH/REUTERS

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka fara musayar fursunonin na Ymemen, wadda ake ganin ba a sake ganin irinta ba tun bayan wadda aka yi na fursunoni sama mutum dubu guda cikin watan Oktobar 2020.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross, ta tabbatar cewa ta mika fursunoni akalla 900 ga iyalansu, tana mai bayyana shirin a matsayin wata gagarumar nasarar da za ta kai ga dawo da zaman lafiya a kasar.

Yemen dai ta fada yaki ne a cikin watan Satumbar 2014, bayan tashin rikici tsakanin da dakarun da ke samun goyon bayan gwamnatin Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi wadanda Iran ke goya wa baya.