An kammala taron AU da mahimman shawarwarin tabbatar da ci-gaban yankin
May 27, 2013A ƙarshen taron ƙolin Ƙungiyar Tarayyar Afirkan da ya gudana a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopiya, shugabanin ƙasashe 54 sun ɗauki mahimman shawarwari waɗanda za su kawo cigaba ga nahiyar, na farko dai sun sanar da girka rundunar soji ta musamman wadda za ta kai ɗauki cikin gaggawa ko da rikici ya ɓarke a ƙasashen yankin, domin rage dogaro kan dakarun ƙetare, haka nan kuma ta bayyana ƙudurinta na ganin kotun hukunta manyan laifukan yaƙi na ICC ta baiwa kotunan nahiyar damar tuhumar shugabanin yankin na su, da kansu.
Shari'ar sabon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda ake sa ran zai bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka na ICC bisa zarginsa da aikata laifukan take haƙƙin bil adama, shi ne ya fi ɗaukar hankali a taron ƙolin shugabanin yankin, inda mahawara ta yi zafi sosai kan hurumin da kotun ke da shi ta yi ta sa baki a lamuran da suka shafi nahiyar.
Matsayin Ƙungiyar Tarayyar Afirka kan kotun ICC
Duk da cewa a lokacin da kotun ta bada sammacin Mr Kenyatta, ƙasar Kenya ta kasa samar da kwamitin shari'ar da zai bincike sa ne, shugabar majalisar zartarwar ƙungiyar, Dlamini Zuma ta ce lokaci ya yi da ya kamata Kotun na ICC ta daina yin kane-kane a abubuwan da suka shafi ƙasashen Afirka
"Bai kamata a ce duk wani abin da ya faru a Afirka a kai shi Kotun ICC ba, kamata ya yi a bari sai dai idan ya gagari kotunanmu na nan Afirka, kuma yanzu da Kenya ta gudanar da sauye-sauye a sashen shari'arta, kuma 'yan ƙasa suka ce sun yi ammana da Kotunan na su, ya kamata a baiwa kotun ƙasar duk wani abu makamancin wannan shari'a."
Shugabanin sun kuma tattauna dangantakarsu da kotun ICC, inda wasu ke kira ga shugabanin da su yanke hulɗa da ita su na bada hujjar cewa shari'arta ba ya wuce tsoffin shugabanin Afirka. Inda shima shugaban ƙungiyar Hailemariam Desalegn, ya yi tsokaci makamancin haka
"Mene ne ICC ke buƙata, mun gaza gane maƙasudin farautar waɗannan shugabanin Afirkan da ta ke yi, a gani na, kamata ya yi ICC ta daina bin shugabanin Afirka kaɗai, a cikin duk waɗanda wannan kotu ta tuhuma kashi 99.9 cikin 100 'yan Afirka ne, wannan na nuna cewa akwai wata matsala da Kotun na ICC"
Kafa sabuwar rundunar tsaron Afirka
Daura da wannan mahawara, shugabanin sun yanke shawarar samar da wata rundunar sojin ta musamman wadda za ta riƙa ɗaukar matakin gaggawa idan rikici ya ɓarke. Bayyanan da suka kai ga wannan shawarar wanda kamfanin dillancin labaran Reuters ya gani sun ce za'a girka wannan runduna ne da gudunmawar sa kai, na sojoji, da makamai daga ƙasashen nahiyar da ke da ƙarfin ɗaukar wannan nauyi.
An Laƙabawa wannan shiri suna African Capacity for Immediate Crisis Response a turance, wanda zai yi aiki a matsayin wucin gadi yanzu, kafin a kammala girka na din din din. Haka nan kuma ana sa ran wannan mataki zai rage dogaron da nahiyar ke yi kan sojojin ƙetare. Sai dai masu fashin baƙi sun ce wannan shiri ya fi shekaru 10 a ajiye ba tare da an aiwatar da shi ba, saboda haka a wannan karon zai iya kasancewa magana ce ta fatar baki kaɗai, kamar dai yadda Andreas Mehler Darektan ƙungiyar GIGA ya bayyana
"Rikicin Mali da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun nuna rashin ƙarfin nahiyar kamar dai yadda aka gani a rigingimun baya. To sai dai a wannan karon wata ƙila ƙasashe mambobi za su faɗaɗa wannan batu su duba yadda zai zauna a siyasance, da yadda zasu sami kuɗin gudanarwa da ma kuma kayayyakin aikin da dakarun zasu buƙata, a tunani na akwai abubuwa da dama da ya kamata su fahimta ko da shi ke ban san irin matakan da suka ɗauka yanzu ba, ko irin waɗanda za su sanya rundunar ta kafu cikin gaggawa ne ba kamar yadda aka gani a baya ba".
To sai dai ana sa ran a wannan karon zai ɗore kasancewar Afirka na daga cikin ƙasashe biyar na farko a jerin ƙasashen da ke ba da gudunmawar sojojinsu ga shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi