1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin AU ya kawo karshe a birnin Yamai

Salissou Boukari MNA
July 8, 2019

An gudanar da taruka masu yawan gaske a fannoni dabam-dabam, kama daga na kungiyoyin ci-gaban farar hula da ci-gaban mata, kiwon lafiya, muhalli, kasuwanci da dai sauransu.

Niger Start Freihandelsabkommen AFCFTA
Hoto: picture-alliance/Xinhua/Z. Yangzi

Tsawon kwanaki hudu da aka shafe ana taron kolin na kungiyar Tarayyar Afirka, an samu halartar dumbun jama'a da suka fito daga sassa dabam-dabam na Afirka, nahiyar Turai da kuma Amirka. Da farko an yi hasashen samun baki kimanin 4000, sai dai ga kiyasin da aka yi taron na birnin Yamai ya samu halartar baki kusan dubu shida. Sai dai ga shugabannin kungiyoyin fararan hula na kasar ta Nijar irin su Maman Nouri na kungiyar ADDC Wadata masu kare hakin masu saye don amfanin yau da kullum da suka halarci zaman taron kungiyoyi da aka yi albarkacin babban taron na Afrika, ya yi tsokaci yana mai cewa.

"Fatanmu a matsayin kungiyoyin masu kare hakin masu amfanin da kaya shi ne kasashen Afirka su fido doka ta hukunta masu cin zarafin al'umma dangane da samar da kayayyaki na bogi.

Hoto: Getty Images/I. Sanogo

Su ma mata sun gudanar da taruka masu yawa albarkacin taron kolin na Tarayyar Afirka, kuma a cewar Madame Kako Fatouma shugabar mata ta kungiyar CONGAFEN wannan taro dai ya bada ba-zata, don haka suna yin jinjina ga magabatan Nijar da sauran shugabannin Afirka da suka halarci taron.

Da yake magana shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka Moussa Faki cewa ya yi duka wannan dawainiya da ake yi burin shi ne na samun Afirka dunkulalliya inda ‘yan Afirka za su yi zirga-zirga tsakanin kasashe ba tare da matsaloli ba, sannan da samun bunkasar tattalin arzikin kasashen na Afirka tare da kiyaye duk wani nau’i na cin zarafin juna.

Kungiyar ta Tarayyar Afirka da ta kammala taron nata da yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Yuli na 2019, ta samu kaddamar da tsarin kasafin kudin tafiyar da kungiyar, da kawo sauye-sauye ga tsarin tafiyar kungiyar, sannan da batun shirya taron tattaunawa tsakanin kungiyar ta Tarayyar Afirka da kungiyoyin yankuna na kasashen Afirka. A karshe kuma taron ya mika godiyarsa ga babban bankin raya kasashen Afrika dangane da ruwa da tsaki da yake yi wajen ganin an cimma buri na hadin kan kasashen Afirka.