1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN KAMMALA TARON SAMAD DA MAKAMASHI MARAS GURBATA YANAYI A BONN.

YAHAYA AHMEDJune 4, 2004

Taron da wakilan kasashe fiye da dari da 54 suka halarrci a birnin Bonn, don tattauna batun samad da makamashi maras gurbata yanayi, watta gagrumar nasara ce ga yunkurin da ake yi na samar da isashen makamashi a duniya. Ministan kare muhallli na tarayyar Jamus, Jürgen Trittin ne ya bayyana haka, a cikin jawabinsa na rufe taron yau a birnim Bonn.

Tutar taron samad da makamashi da za a iya ssabuntawa da aka yi a Bonn.
Tutar taron samad da makamashi da za a iya ssabuntawa da aka yi a Bonn.

A yau ne aka kawo karshen taron kasa da kasa kan samad da makamashi maras gurbata yanayi, da gwamnatin tarayyar Jamus ta shirya ta kuma karbi bakwancinsa a nan birnin Bonn. Taron, wanda aka shafe kwana 4 ana yi a zauren muhawarar tsohuwar majalisar dokokin tarayya ta Bundestag, ya sami halartar wakilai fiye da dubu 3 daga kasashe dari da 54 na duniya.

Da yake jawabin rufe taron bayan wakilan sun kammala tattaunawar da suke yi, ministan kare muhalli na tarayya, Jürgen Trittin, ya kwatanta ganawar da wakilan kasashen duniya suka yi da juna a nan birnin Bonn tamkar wata gagarumar nasara, inda wannan shi ne karo na farko da aka taba zama tare, don tattauna wannan batun makamshi da ya shafi kasashen duniya baki daya, wato da masu tasowa, da kuma masu ci gaban masana’antu. Ministan dai ya nanata cewa, yanzu ba a kan jawabai kawai za a tsaya ba. Kamata ya yi duk kasashen da suka halara a wannan taron, su shiga aiwatad da kuduroin da aka zartar nan take, idan wakilansu sun gabatar wwa gwamnatocinsu irin sakamakon da taron ya haifar. Minista Trittin, ya kuma jadadda aniyar gwamnatin Jamus, ta ganin cewa an cim ma nasara a wannan gurin. Gwamnatin tarayya dai za ta ci gaba da gudanad da bincike a nan cikin gida, don a kai ga matsayin da, za a iya samo makamashi daga iska alal misali, wanda tsadarsa ba zai wuce santi 30 na Amirka, a ko wace Kilowatt daya ba, inji ministan.

Ban da hakan, gwamnatin ta kuma ware kudi na fiye da Euro biliyan daya, don bunkasa wannan fasahar, ta samad da makamashi a sawwakaken hanya, don duk al’ummomi musamman ma na kasashe matalauta su sami damar yin amfani da shi, don kyautata halin rayuwarsu.

A cikin nata jawabin, ministan ma’ammalarr tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta ce, batun samun makamashi, shi ne ya zamo babban abin da ke kalubalantar duk kafofin siyasa a cikin wannan karnin. Gurin gamayyar kasa da kasa ne ganin cewa, an samar wa mutane fiye da biliyan daya a duniya, hanyar yin amfani da makashi, wanda kuma ba shi dauke da ko kuma zai iya janyo musu wata illa.

Bayan wakilan sun fito daga babban zauren taron ne na sami damar tattaunawa da ministan makamashi da ma’adinai na Jumhuriyar Niger, malam Rabi’u Hassan Yari, wanda yake cikin tawagar da Firamiyan kasar Hamma Amadou, ya yi wa jagoranci zuwa taron.

Duk mahalartan dai sun nuna gamsuwarsu da yadda gwamnatin tarayyar Jamus ta shirya taron.