1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maroko ta lashe kofin Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
September 1, 2025

Kasar Maroko ta lashe kofin kwallon kafa na Afirka ba masu wasa a gida. Shararren dan wasan kwallon kwando Jeremy Lin ya bayyana yin murabus, ko ya ta kaya a wasannin da aka fafata a karshen mako a lig-lig na Turai?

Maroko ta lashe gasar cin kofin Afirka
Maroko ta lashe gasar cin kofin AfirkaHoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

A gasar Bundesliga ta Jamus da aka fafata wasa mako na biyu a karshen mako, inda za a iya cewa kungiyar kwallon kafa ta Bayer Leverkussen ba ta fara kakar ta bana da kafar dama ba. Bayan kashin da ta sha a hannun Hoffenheim a gida a wasan mako na farko da kuma canjaras din da ta yi da Werder Bremen uku da uku a mako na biyu, kungiyar ta saitawa sabon mai horas da 'yan wasanta layi. Da sanyin safiyar Litinin daya ga wannan wata na Satumbar 2025 ne dai, rahotanni suka bayyana cewa Bayer Leverkussen ta kori Erik Ten Hag da ya kama aiki a watan Agustan da ya gabata. Korarren mai horas da 'yan wasan Manchester United, Ten Hag ya canji Xabi Alonson da ya ja ragamar Leverkussen din ta lashe gasar Bundesliga a karon farko tun kafa ta a kakar 2023 zuwa 2024 tare da kammala kakar bara a matsayi na biyu. Alonson dai, ya koma kungiyar Real Madrid ta Spaniya.

Karin Bayani: Gasar cin kofin CHAN na Afirka cikin Labarin Wasanni

Wasan Augsburg da. Bayer Munich na Bundesliga na JamusHoto: Alexander Hassenstein/Getty Images

A sauran wasannin Bundesliga kuwa za a iya cewa Bayern Munich ta sake fara kakar wasan ta bana da kafar dama, inda dan wasan da ta cefano daga Liverpool Luiz Diaz ke nuna bajinta. A gefe guda a iya cewa Borussia Dortmand da ke da maki hudu, na laliben yadda za ta kai ga wannan kambu a karkashin mai horas da 'yan wasanta Niko Kovač da ya taimaka mata ta karkare kakar wasannin ta bara a matsayi na hudu da kyar da jibin goshi. A wasannin na karshen mako dai St. Pauli ta bi Hamburg har gida ta lallasa ta da ci biyu da nema. A bana ne dai Hamburg din ta farfado daga rukuni na biyu, bayan kwashe shekaru da fadawa. Sai dai ko za a iya cewa, ba ta shirya ba ta dawo? Sabanin Hamburg din, takwararta FC Cologne da suka dawo rukunin Bundesliga na farko a bana tare na bayar da mamaki. A wasanta na farko dai, ta bi Mainz har gida ta lallasa ta da ci daya mai ban haushi, yayin da ta karbi bakuncin Freiburg a mako na biyu, ta kuma yi mata cin yankan kauna hudu da daya.

Frankfurt ta bi Hoffenheim har gida ta caskara ta da ci uku da daya, RB Leipzig kuwa ta karbi bakuncin Heidenheim ta lallasa ta da ci biyu da nema kamar yadda Stuttgart ta karbi bakuncin Borussia Mönchengladbach ta casa ta da ci daya mai ban haushi. Bayern Munich kuwa ta bi FC Ausgburg har gida ta yi mata dukan kawo wuka da ci uku da biyu kana Borussia Dortmund ta karbi bakuncin Union Berlin ta lallasa ta da ci uku da nema, an kuma tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Wolfsburg da Mainz.

Maroko ta lashe gasar cin kofin Afirka, inda Gianni Infantino shugaban FIFA, da Shugaba William Ruto na Kenya gami da Patrice Motsepe shugaban hukumar kwallo ta AfirkaHoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Kasar Maroko ta lashe gasar cin kofin kasashen Afirka masu buga wasa a gida na kwararru karo na uku bayan doke kasar Madagaska a wasan karshe da aka kara ranar Asabar da ta gabata a birnin Nairobi na kasar Kenya. Morokon dai ta samu nasara da ci 3 da 2, nasarar kuma ta nuna yadda kasar ke ci gaba da nuna tasiri a wasannnin kwallon kafa na kasashen Afirka.

Bayan kwashe tsawon shekaru tara ana fafatawa da shi a fagen kwallon kwando, shararren dan wasan kwallon kwandon Jeremy Lin ya bayyana yin murabus a shafinsa na Instagram. Lin ya wallafa cewa: "Ya kasance abin alfahari a rayuwata, fafatawa a fagen wasa da kwararrun da suka shahara cikin kalubale da duniya ba ta taba tsammanin dan wasa kamar ni zai iya ba.

Dan kasar Australia Alex De Minaur da ke kara wasan Tennis mai tasiri na US-Open karo na uku a jere, ya ce zai ci gaba da gwada sa'a. A wannan karon ya kai zuwa mataki na uku, abin da ke nuna irin shirin da dan wasan na Australia ya yi.

Haka Jannik Sinner da Iga Swiatek suna cikin wadanda suka nuna gwaninta a karshen mako, inda suka kai mataki na gaba a gasar ta Tennis ta US-Open da ke wakana a kasar Amurka. Sai dai duk 'yan wasan biyu sun kai mataki na gaba ta hanyar tsallake rijiya da baya, lamarin da ke nuna halin da gwanaye suka samu kansu a gasar ta Amurka.

Novak Djokovic a wajen wasan Tennis na US-OpenHoto: Corinne Dubreuil/ABACAPRESS/IMAGO

Akane Yamaguchi ta doke tsohuwar 'yar wasan kwallon badminton da ke matsayi na daya a jadawalin gasar a duniya Chen Yufei ta Chaina da ci 21-9 da 21-13 a Lahadin karshen mako, a bin da ya ba ta damar samun nasarar lashe wasan karshe na gasar kwallon badminton din ta duniya da ta gudana a birnin Parsi na Faransa. 'Yar kasar Japan din Yamaguchi ta samu nasarar cikin mintuna 37, inda ta samu kofin zinarenta na uku a gasar. Dama dai, Yamaguchi din ce ta lashe gasar a shekara ta 2021 da 2022.

Dan kasar Habasha Hailemaryam Kiros da 'yar kasar Holland Sifan Hassan sun samu nasara a gasar gudun fanfalake ta duniya bangaren mata da maza da aka gudanar a birnin Sydney na kasar Australiya. Kiros ya samu nsarar kammala gudun a sa'o'i biyu da mintuna shida da dakika shida, abin da ya sa ya zama na biyu a tarihi da ya kammala gasar ta birnin Sydney cikin sauri. Mai shekaru 28 a duniya, dan kasar Habashan ya kammala tseren dakika 10 tsakaninsa da dan uwansa Addisu Gobena yayin da dan kasar Lesotho Tebello Ramakongoana ya kammala a matsayi na uku.

A nata bangaren Sifan Hassan ta kammala tseren na gudun fanfalaken a sa'o'i biyu da mintuna 18 da dakika 22, mintuna kusan uku tsakaninta da 'yar kasar Habasha Workenesh Edesa da ta kafa tarihi a bara. 'Yar kasar Kenya Brigid Kosgei ta kammala a matsayi na biyu bayan Hassan da tsiran dakika 34, yayin da Edesa ta kammala a matsayi na uku.