1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kasshen duniya na tururuwar shiga kungiyar Brics

Binta Aliyu Zurmi
August 22, 2023

Shugabannin kungiyar Brics da suka hada da Brazil da Rasha da China da Indiya gami da Afirka ta Kudu mai masaukin baki na gudanar da taron su karo na 15 a birnin Johannesburg karkashin taken "Brics da Afirka"

Südafrika BRICS-Gipfel
Hoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

A ranar farko ta taron kungiyar Bricks, Shugaba Cyril Ramaphosa mai masaukin baki kuma shugaban kungiyar na yanzu ya ce wannan babbar rana ce ta tarihi. A jawabinsa ya bayyana nasoririn da kungiyar ta samu ya zuwa yanzu.

 "Sauye-sauyen da aka samu a tattalin arzikin BRICS cikin shekaru 10 da suka gabata, ya taimaka matuka wajen sauya fasalin tattalin arzikin duniya. Kasashen BRICS su ne kashi daya bisa hudu na tattalin arzikin duniya, kashi na biyar na cinikayyar duniya, kuma kungiyar na wakiltar fiye da kashi 40 cikin 100 na al'ummar duniya."

Taron na kwanki uku da bai sami halarta shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ba ya mayar da hankali a kan bukatar kasashen duniya sama da 50 da ke neman zama mambobin da ma lalubo sabuwar turba ta gudanar da ayyukan kungiyar.

Tasirin kungiyar da a baya ake yi wa kallon mara katabus, sakamakon babakeren kasashen yamma yanzu haka Brics na kara habbaka.

Najeriya da Saudi Arabiya da Iran da Argentina na daga cikin sabbin kasashen da ke neman a sahale musu zama mambobin Brics.

China da ke zama babbar abokiyar cinikayyar kasashen Afirka, a taron na yau ta yi alkawarin samar wa kasashen Afirka kayayaki masu inganci, biyo bayan zarginta da ake yi mata na rashin adalci a yayin samar da kayayaki ga sauran bangarorin duniya.