Tsawata wa'adintattauna nukiliyar Iran
June 30, 2015Talla
A baya dai kasashen da ke tattauna rikicin nukiliyar sun tsayar da wa'adin daren Talata na cimma yarjejeniyar, wanda ke da nufin dakatar da shrin nukiliyar Iran, kana ta samu sakayyar cire mata takunkumi.
A matsayin sharar fage na ganin cewa an cimma wannan manufa dai, tuni Kungiyar Tarayyar Turai da da Amurka suka dakatar da wasu takunkumi da ke kan Iran, a yayin da Tehran a nata bangare ta fara rage ayyukan da take yi a cibiyar nukiliyarta tun 2013, bisa ga kwaryakwaryar yarjejeniyar da aka cimma.
Har yanzu dai bangarori biyun na da sabanin ra'ayi dangane da cire wa Iran din dukkan takunkumi, kuma ko za'a bar jami'an bincike na hukumar makamashi na duniya su ziyarci yankuna sojin kasar.