1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa ya ki cinyewa a Senegal

Abdourahamane Hassane MAB
March 10, 2021

Masu fafutuka a Senegal a bisa jagorancin madugun adawa Ousmane Sonko sun yi kiran wata zanga-zanga a ranar Asabar don ganin an sako fursunonin siyasa, duk da jawabin da shugaba Macky Sall ya yi na a kwantar da hankula.

Senegal Justiz l Protest von Unterstützern von Sonkoin Dakar
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS


Tun da farko masu gangamin sun soke zanga-zangar da suka shirya yi a ranar Asabar bayan sakin da aka yi wa dan adawa Ousmane Sonko wanda ya shafe kusan kwanaki hudu a tsare, kafin da daga bisani a gabatar da shi a gaban alkali, kuma ya sake shi a kan belli sakamakon zargin da ake yi masa na yi wa wata mata fyade.

Kasar ta Senegal wacce ake yi wa kallon daya daga cikin kasashen Afirka na Yamma masu bin sahihin tafarki na dimukaradiyya, wacce kuma ta kwashe shekaru da dama cikin kanciyar hankali, a karon farko gwamnati ta baza sojoji kan tituna domin murkushe masu bore. Da yake yi jawabi ga 'yan kasar ta Senegal Macky Sall ya yi kira da a kwantar da hankula.

Macky Sall ya fara sara yana duban bakin gatari bayan boren adawaHoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/D. Gueye

Shugaba Sall ya ce: "Ina fahimtar ku al'ummar kasata, fushin da ku bayyana a kwanakin baya-baya nan yana da nasaba da matsala ta tattalin arziki mafi muni da ake fuskanta saboda annobar COVID-19 a duniya, babu wata kasa da ta sha daga wannan matsalar ta tattalin arziki har ma da kasarmu, wacce ta janyo dubban jama'a suka rasa ayyukansu ,iyalai da dama sun fada cikin talauci da fargaba da kuma takaici."


Sai dai Ousmane Sonko wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa wanda yake ganin zai iya kalubalantar Macky Sall a zaben shugaban kasa na 2024 na ganin cewa ana neman yi masa zango kasa domin hana shi tsayawa takara a zaben. Saio bayan sakin shi ya yi kira ga al'ummar da su sake fitowa a ranar Asabar domin kwatar 'yanci na dimukaradiyya cikin ruwan sanyi ba tare da haddasa wani ta'addi ba a kan dukukiyoyin kasa da na jama'a ba.

Dan adawa Ousmane Sonko ya zama farin wata a fagen siyasar SenegalHoto: DW/R. Ade

Sonko ya ce: "Zuwa gare ku al'ummar Senegal musammun ma matasa, ka da ku yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da yin tsayin daka, ka da ku yi sake da wannan dama domin ba za mu bari ba, mu samu asarar rayuka ba tare da cimma nasara a kan bukatunmu ba, a ci gaba da yin gangami amma dai cikin lumana."

Mutane guda biyar ne suka mutu a sakamakon gangamin yayin da aka samu asara mai yawa ta dukiyoyi da kadarori na jama'a masu zaman kansu da kuma mallakar gwamnati. Shugaba Macky Sall ya sha alwashin taimaka wa wadanda suka yi asara da ma wadanda suka jikkata, inda ya ce gwamnati za ta dauki nauyin kula da su, sannan ya yi sasauci ga dokar hana fita, ya kuma ce a shirye yake a tattauna da shi.