An kashe dalibai a wata makarantar Rasha
May 11, 2021Hotunan da shaidun gani da ido suka saki a shafukan sada zumunta sun nuna yadda dalibai ke tsalle daga tagogin ginin mai hawa uku don tsira da rayukansu. Jami'an yankin sun fada wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa wasu mutane 20 galibin su yara na kwance a asibiti sakamakon mummunan rauni da suka ji.
Hukumar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar Rasha ta bayyana cewa ta kashe mutun daya, sannan ta kame matashi mai shekaru 19 da ake zargi da aikata wannan harbin kan mai uwa da wabi. Wannan dai na zama harbe-harbe mafi muni da aka gudanar a wata makaranta ta kasar Rasha a cikin shekaru na baya-bayannan.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba da umarnin sake duba dokokin da suka shafi mallakar makamai da kuma harkar tsaro a makarantun kasar.