An kashe dalibai da malamai a Siriya
October 27, 2016Talla
Kungiyoyin da ke sa ido a Siriya sun ce 'yan tawaye na amfani da makaman roka a yayin mai da martanin kan sojojin gwamnati da na kawancensu na Rasha da ke kaddamar da sumamae a yankunansu, wanda hakan ke yin mumunar Illa ga rayuwar fararen hula da ke yammacin birnin na Aleppo.
Wannan sabon harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar kula da kanana yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce ta samu rahotannin da ke zargin jiragen kawancen yakin Siriya da na Rasha sun kashe kananan yara 22, tare da hallaka malamai da dama a wani makaranta da ke lardin Idib. To sai dai Rasha ta yi Allah wadai da wannan zargi.