Burkina Faso: An hallaka fararen hula
July 18, 2022Talla
Wasu gwamman fararen hulla sun gamu da ajalinsu a Burkina Faso sakamakon wani harin ta'addanci a lardin Yagha mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Majiyar tsaro ta tabbatar wa manema labarai cewa maharan sun kuma kwashe abinci da dabbobin al'ummar yankin da suka kai wa harin na daren Lahadi.
Kamar sauran makwabtanta Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso na fuskantar hare-haren 'yan bindiga masu ikrarin jihadi, inda kawo yanzu kaso 40 cikin dari na kasar baya hannun gwamanti.