An kashe masu taimaka wa sojoji a Burkina Faso
May 16, 2022Talla
Harin ya rutsa da 'yan kato da gora da wasu fararan hular a gundumar Guessel da ke a yankin arewaci. Bayan da aka samu saukin hare-hare a tsawon makwanni, a halin yanzu gwamnatin mulkin sojan ta Damiba na fuskantar karuwar hare-haren wanda aka kiesta cewar a kasa da makwanni uku mayakan jihadi sun kashe fararen hula da sojoji sama da dari.