Burkina Faso: Harin ta'addanci ya rutsa da farar hula
August 5, 2021Talla
Majiyoyin tsaro sun ce an samu gawarwaki mutane da yawa a cikin kauyuka wadanda masu jihadi suka yi wa yanka rako. Yan ta'addar sun kai hare-haren nea kauyukan Banogo da Basian da Tokabangou da Gadba da kuma Pensa da ke kan iyaka da Nijar, majiyoyin sun ce a harin masu jihadin sun kashe 'yan kato da gora da dama wadanda ke tallfa wa sojoji a cikin aikin kula da tsaro.