1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kashe gomman mutane a Burkina Faso

August 26, 2024

Mutanen da aka halaka sun je su taimaki sojoji gina ganuwa ne domin kare garin Barsalogho daga mahara.

Wani kauye a Burkina Faso
Wani kauye a Burkina FasoHoto: Michele Cattani/AFP/Getty Images

'Yan Ta'adda sun halaka mutane da dama ciki har da fararen hula a Burkina Faso kamar yadda jami'an tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Tun a shekarar 2015 'yan bindiga masu alaka da Al-Qaeda da kuma IS suka fara kai hari a Burkina Faso inda suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da matsugunnansu.

'Yan ta'adda sun kona ofishin likitocin agaji a Burkina Faso

Harin na baya-bayan nan ya auku ne ranar Asabar a kauyen Barsalogho da ke arewa ta tsakiyar kasar.

Wani jami'in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce akwai karin wasu mutane da suka rasu ciki harda jam'an tsaro kuma da yawa sun ji raunuka sannan an kai su wani asibiti da ke garin Kaya mai nisan kilimita 45 daga babban birnin kasar.

Burkina Faso: Damuwa kan kashe fararen hula

Wani mazaunin kauyen ya fadawa manema labarai cewa akasarin wadanda aka kashe matasa ne da suka je taimaka wa sojoji gina ganuwa a garin domin kare su daga kungiyoyin 'yan ta'adda.