1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe Abu Hassan al-Hashimi al-Qurashi

Abdourahamane Hassane
November 30, 2022

Kungiyar IS ta sanar da cewar an kashe jagoranta Abu Hassan al-Hashimi al-Qurashi tare da bayyana cewar an kasheshi ne a lokacin da yake yaki da makiyan Allah.

Afghanistan | Al Kaida Kämpfer
Hoto: AFP/Getty Images

A cikin wani sakon videon da ya fitar, kakakin kungiyar masu jihadin Abu Umar al-Muhajir, ya sanar da cewar an nada sabon khalifan  Abu Al-Hussein al-Hussein al-Qurashi. A baya baya nan dai Kungiyar ta IS ta kwashi kashinta a hannu a kasashen Iraki da Siriya. An kashe shugaban IS na farko, Abu Bakr al-Baghdadi al-Qurashi a wani harin da Amirka ta kai a Syria a shekarar  ta 2019, kuma an kawar da magajinsa, Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurashi a watan Fabrairu da ya gabata a wani farmakin da dakarun Amirka na musamman suka kai a arewa maso yammacin Siriya.