Najeriya : Jami'an tsaro 19 sun mutu
March 9, 2022
Talla
Wata majiyar tsaro da ta tabbatar da labarin ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa, harin ya auku ne a garin Kanya na jihar Kebbi mai makwaftaka da Jamhuriyar Nijar a wannan Talata.
Kana kuma harin na wannan Talatar na zuwa ne kwana daya bayan wani kazamin harin da 'yan bindiga suka kai kan 'yan vigilantes da fararen hulla a yankin, inda suka kashe gwamman mutane.