1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe Komandan 'yan tawayen Libiya

July 29, 2011

Sojojin shugaba Moammar Gadhafi sun kashe komandan askarawan 'yan tawayen Libya Abdel Fattah Younes, da kuma wasu muƙarrabansa guda biyu, akan hanyarsa ta zuwa Benghazi.

'Yan tawayen Libya ɗauke da tutar ƙasarsuHoto: dapd

. 'Yan tawayen ƙasar Libya sun bayanna cewa dakarun Moammar Gadhafi sun hallaka komandan askarawansu Abdel Fattah Younes da kuma biyu daga cikin masu tsaron lafiyarsa. Sojojin na Gwamnatin sun yi nasarar harbe  Younes ne akan hanyarsa ta zuwa taron da ya  shafi harkokin tsaro  na 'yan tawaye a birnin Benghazi.  Shi dai Abdel Fatah Younes ya riƙe muƙamin ministan tsaro a cikin gwamnatin Moammar Gadhafi kafin ya juya masa baya a watanni biyar da suka gabata.

 Shugaban majalisar riƙon ƙwarya ta  Libya da wasu ƙasashen duniya suka amince da ita wato Mustafa Abdel Jalil ya nunar da cewa askawaransu sun tsafke waɗanda suka kashe Younes. Tun da farko dai 'yan tawayen sun yi iƙirarin ƙwace birnin Ghezala daga hannun sojojin Gadhafi tare da mayar da shi ƙarkashin kulawarsu. kana sun sha alwashin fatattakar sojojin gwamnati daga wasu garurzwa huɗu da ke wannan yanki mai yawan tsaunuka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman