1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe manyan jami'an gwamnatin Siriya

July 18, 2012

Ministan tsaron ƙasar Siriya da surukin shugaba Assad na daga cikin mutanen da suka rasu a wani harin kunar baƙin wake a birnin Damaskus.

An undated handout photo distributed by Syrian News Agency (SANA) on July 9, 2012 shows Deputy Prime Minister and Defence Minister Dawoud Rajha (C) attending with other officials a Syrian air defence live ammunitions exercise in an undisclosed location. REUTERS/SANA/Handout (SYRIA - Tags: MILITARY POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Ministan tsaron ƙasar Siriya Daoud Rajha da muƙaddashinsa Assef Shawkat dake zama surukin shugaban ƙasa Bashar al-Assad sun rasu a wani lamarin da tashar telebijin ɗin ƙasar ta kira harin ta'addanci a cikin ginin ma'aikatar tsaron ƙasa dake birnin Damaskus. Ministan cikin gida Mohammed Ibrahim al-Shaar na daga cikin mutanen da suka samu munanan raunuka a fashewar wani bam a cikin ginin. Masu fafatuka sun ce wani ɗan ƙunar baƙin wake na ƙungyiar 'yan tawaye ta Free Syrian Army ya kai harin, wanda ya faru lokacin da ministocin gwamnati da manyan jami'an tsaro ke wani taro a cikin ginin dake unguwar Rawda. Harin dai ya zo a daidai lokacin da aka shiga kwanaki huɗu a jere ana mummunan artabu tsakanin dakaru masu biyayya ga shugaba Assad da 'yan tawaye a Damaskus. A wannan Larabar kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya zai kaɗa ƙuri'a akan wani daftarin ƙuduri mai samun goyon bayan ƙasashen yamma dake barazanar sanya takunkumi a kan gwamnatin Assad.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas