An kashe masu zanga-zanga a Masar
July 26, 2013Talla
A birnin Alexandriya da ke a yankin arewacin ƙasar an kashe mutane guda biyu a fadan da aka gwabza tsakanin sassan biyu. Nadiya El Abbas wata mai goyon bayan Mursi ce da ta halarci gangamin daga yankin arewacin ƙasar.
Ta ce : ''Mun zo ne nan, domin nuna goyon baya ga cikkaken shugaba,ta ce ba za mu amince da wani shugaba ba,domin Mursi shi ne shugaban da muka zaɓa.'' A share ɗaya kuma masu neman sauyi sun riƙa raira kallamun nuna ƙemar tsohuwar gwamnatin tare da jinjinawa hukumomin sojin da suka yi juyin mulki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar