An kashe mayaƙan Ƙungiyar IS 18 a Libiya
June 10, 2015Talla
A Libiya a wannan Laraba mayaƘan ƙungiyar 'yan jihadi ta IS 18 sun hallaka a cikin wani ƙazamin faɗan da ya haɗasu da mayaƙan wata ƙungiya ta masu kishin islama a garin Derna da ke a gabascin ƙasar ta libiya.
Wasu shaidun gani da ido da ke a garin na Derna sun ruwaito cewa faɗan ya ɓarke ne a marecen Talata bayan mutuwar Salem Derbi shugaban Ƙungiyar Majlis al-Choura ta masu kishin islama na asar ta Libiya wanda mayaan IS suka kasheshi bayan da ya i ya yi mubayi'a ga jagoran Ƙungiyar IS Abu bakr al Bagdadi.