1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: An kashe mayakan al-Shabaab 37

Abdul-raheem Hassan MNA
November 20, 2018

Jiragen yakin Amirka sun kaddamar da samame a sansanonin mayakan da ke Arewa maso gabashin babban birninn kasar Mogadishu, inda aka kashe 'yan kungiyar 37.

Somalia Al-Shabab-Kämpfer
Hoto: Getty Images/AFP/M. Abdiwahab

Babu rahotannin asarar rayukan fararen hula yayin artabun tsakanin dakarun gwamnati da mayakan. Dakarun kawancen Amirka da sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka AU tare da sojojin Somaliya na ayyana cin galaba kan kungiyar al-Shabaab.

Kungiyar al-Shabaab ta sha kaddamar da hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro da gine-ginen gwamnati da zimmar kafa daular musulunci a Somaliya.