1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane 34 a Najeriya

Abdourahamane Hassane
March 22, 2022

Akalla mutane 34 da suka hada da sojoji biyu ne aka kashe sakamakon wasu hare-hare da aka kai a arewa maso yammacin Najeriya a kauyuka hudu da ke yankin Kaura.

Nigeria Gefängnisausbruch in Owerri
Hoto: David Dosunmu/AP Photo/picture alliance

Akalla mutane 34 da suka hada da sojoji biyu ne aka kashe sakamakon wasu hare-hare da aka kai a arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana. Sojoji biyu na cikin mutane 34 da aka kashe” a hare-haren da ‘yan bindiga da ba a tantance ba suka kai a kauyuka hudu da ke yankin Kaura, in ji kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan.