An kashe mutane a cikin wata zanga zanga a Iraki
April 23, 2013An dai sha artabu ne tsakanin jama'ar yan sunni masu yin addawa da gwamnatin fira minista Nuri Al Maliki, da kuma jami'an kwantar da tarzoma a arewacin birnin Bagadaza.
Jami'an tsaron dai sun afkawa wani gungun masu yin gangamin a garin Houweijah da ke a yammancin birnin Kirkouk, da ke yin wata zanga zanga tun makonni da dama da suka wuce inda suka buɗe masu wuta. Ofishin ministan cikin gida na ƙasar ya ce sojojin sun kai harin ne, bayan da wa'adin da gwamnatin ta giciyawa yan sunni na su miƙa wanda ya kashe wani soji gwamnatin a yankin a makon jiya ya kawo ƙarshe.Tun a tsakiyar watan Disamba da ya gabata yan ɗarikar Sunni ke ta gudanar da jerin zanga zanga a yankin arewaci na kasar, domin matsa ƙaimi ga shugaban gwamnatin da ya yi marabus.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman