An bude wuta a gidan tarihin Yahudawa a Washington
May 22, 2025
Wani dan bindiga ya bude wuta kan dandazon jama'a a wani taro a gidan adana kayan tarihi na Yahudawa a birnin Washington a Amurka, rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane biyu ciki har da wani jami'in diflomasiyyar Isra'ila. Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba.
"Abin da na sani shi ne, wannan mummunan lamari zai firgita jama'a da dama, kuma ina so in bayyana cewa ba za mu amince da wannan tashin hankali ko kiyayya a ba. Ba za mu yarda da duk wani ta'addanci ba, kuma za mu yi tsayin daka don aikewa da sako karara cewa ba za mu amince da kyamar Yahudawa ba." Muriel Bowser, mai rike da mukamin magajin garin birnin Washington.
Karin bayani:Dan bindiga ya kashe mutum uku a Amirka
Jami'an tsaro sun kama matashi mai shekaru 30 da ake zargi da kai harin. Wakilin Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya dangaantaa harin da ta'addanci na kyamar Yahudawa.
Da yake martanin alhini kan mumunar harin cikin gaggawa a shafukan sada zumunta, Shugaba Donald Trump ya ce "Dole a kawo karshen irin wadan nan akidu yanzu. Kiyayya da tsattsauran ra'ayi ba su da gurbi a Amurka,"