An kashe mutane a wata masha a Kamaru
September 15, 2026
Talla
Hukumomi sun ce harin ya faru ne da yammacin Litinin, amma ba su bayyana wadanda suka kai harin ba zuwa yanzu. Yankunan da ake magana da Ingilishi a Kamaru sun shafe kusan shekaru goma suna fama da rikici tsakanin jami'an gwamnati da kungiyoyin masu neman ballewa wato Ambazoniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 6,000 sun mutu tun bayan barkewar rikicin, yayin da daruruwan dubban mutane suka rasa matsugunansu a Kamaru. A shekarar 2025, sama da mutane 100,000 sun tsere daga kasar zuwa Najeriya saboda rikicin.