1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe rayuka a gabashin kasar Kwango

May 10, 2022

Wasu hare-hare a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun salwantar da rayukan gomman mutane da ke kokarin tsere wa rikici. Bayanai sun ce maharan sun yi wa wasu yankan rago.

DR Kongo weitere Tote nach einem Massaker bei Ituri
Hoto: Jorkim Jotham Pituwa/AFP via Getty Images

Sama da mutum 70 galibin su mata da kananan yara ne wasu 'yan bindiga suka halaka a wasu hare-hare biyu a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Hukumomi a kasar sun ce maharan sun afka wa garin Kablangete ne da ke a lardin Ituri inda suka kashe akalla mutum 50.

Haka zalika sun ce wasu daga cikin maharan kungiyar CODECO, sun far wa mazauna kauyen Bikilisende mai tazarar kilomita bakwai inda can ma suka salwantar da sama da mutun 20.

Wasu da suka tsallake rijiya da baya, sun ce maharan sun yi wa mutane ciki har da jarirai yankan rago.

Bayanai na kuma cewa akwai sama da mutun 100 da suka bata a hare-haren biyu.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Kwangon, sun ce sun kwashe wasu daga cikin wadanda suka yi matukar jikkata a hare-haren.