An kashe shugaban Taliban na Pakistan
November 1, 2013Talla
Wani jami'in tsaron Pakistan din da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce shugaban na Taliban Hakimullah Mehsud ya gamu da ajalinsa sakamakon harin da jirgin yakin na Amurka ya kai, a inda ya ke a arewacin Waziristan.
A da dai an sha bayyana cewar an hallaka Mehsud, sai kuma daga baya ya bayyana. To amma a wannan karon jami'an na tsoron Pakistan, sun ce tabbas madugun na 'yan Taliban din ya riga mu gidan gaskiya.
Ita ma dai kungiyar Taliban a Pakistan, ta tabbatar da mutuwar jagoran na ta, har ma ta bayyana cewar za a yi masa jana'iza a gobe Asabar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita:Usman Shehu Usman