An kashe sojoji a Libiya
July 23, 2017Talla
Ricikin dai ya faru ne a dai dai lokacin dakarun ke kokarin dannawa zuwa sauran yankunan da mayakan tarzoma ke ci gaba da turjiya, musamman ta gabashin fadar gwamnatin kasar. Rahotanni sun kuma ce dakarun sun yi barin wuta ta sama a kan mayakan tarzoma da ke birnin Derna.
Shi dai Khalifa Haftar mayaki ne na marigayi shugaba Muammar Gaddafi da aka kashe a shekara ta 2011, wanda kuwa daga bisani ya juya masa baya. Haftar yana kuma samun goyon baya ne yanzu daga kasashen Masar da hadaddiyar daular larabawa a gwagwarmayar da ya ke jagoranta na kashin kai a Libiyar.