1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan ta'adda sun halaka sojojin Mali

March 5, 2022

Wata majiya ta ce sojojin Mali ba su nemi dauki daga sojojin Faransa na Barkhane ba domin tuni Faransa ta umurci sansanin sojojinta da ke kusa da inda aka kai harin da ya dakatar da ayyukansa.

Symbolbild Burkina Faso  Mehr als 138 Tote bei Anschlag
Hoto: Michel Cattani/AFP

Wani harin mayaka masu ikirarin jihadi a wani barikin soji da ke tsakiyar kasar Mali ya yi ajalin rayukan sojoji 27 da kuma halaka 'yan ta'adda 47. Rundunar sojin Mali wace ta sanar da haka a cikin wata sanarwa, ta ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Jumma'a. Ta kuma ce artabu ne da ya raunata sojoji da 'yan ta'adda da dama. 

Wata majiya ta sojin Faransa da ba ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran na AFP sunanta ba, ta ce adadin sojoji da 'yan ta'adda da suka rasa rayukansu ma zai iya zarta alkaluman da sojojin Mali suka sanar.