An kashe wani sojan Amirka a Bagadaza.
June 7, 2006Talla
A wata sabuwa kuma, Hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqin, ta ba da sanarwar mutuwar wani sojanta, sakamakon raunin da ya ji yayin da wani bam da aka dasa a gefen titi a birnin Bagadaza ya tashi, kusa da motar da rukuninsa ke sintiri a ciki.
Hakan dai ya kawo adadin yawan dakarun Amirka da suka rasa rayukansu a Iraqin tun afka wa ƙasar da aka yi a cikin shekara ta 2003, zuwa dubu 2 da ɗari 4 da 77, bisa alƙaluman da kamfanin dillancin labaran nan AFP ya samo daga ma’aikatar tsaron Ammirkan, wato Pentagon.