1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wasu sojojin Najeriya

December 16, 2018

Wata nakiya da ake zargin Boko Haram ta dana, ta kashe wasu sojojin Najeriya a jihar Borno da ke arewacin kasar. Sojin Najeriya dai na fama da hare-haren 'yan tarzoma a baya-bayan nan.

Symbolbild Nigeria Armee
Hoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa akalla sojojin kasar biyu ne suka mutu sakamakon tashin wata nakiya a gefen hanya, kamar dai yadda wata majiya ta tsaro ta tabbatar.

Sojojin na aikin sintiri ne cikin jerin gwanon motoci a garin Gamboru na jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin kasar, garin da ke iyakan Najeriyar da Kamaru.

Yankin dai, yanki ne da 'yan kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau ke da karfi a ciki, kuma an saba yi wa sojojin irin wannan takon lokacin da suke sintiri.

A share guda kuwa daya bangaren kungiyar mai alaka da kungiyar IS, ya kai wani harin da yammacin Juma'ar da ta gabata a sansanin soji da ke Gudumbali cikin gundumar Guzamala, sai dai sojojin sun murkushe mayakan ba tare da labarin rasa wani jami'i ba.