Dan shekaru 13 ya hallaka Yahudawa bakwai
January 28, 2023Binciken farko ya tabbatar da cewa, Bafalasdinen da ya bude wuta a daf da wani ginin bautar Yahudawa, dan shekaru goma sha uku ne da haihuwa, harin da Isra'ila ta ce shi ne mafi muni da ta gani a shekarun baya-bayan nan, ya hallaka mutum akalla bakwai tare da raunata wasu uku, kafin daga bisani yan sanda su harbe matashin har lahira. Daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu a kazamin harin na daren Jumma'ar da ta gabata, har da wata dattijuwa 'yar shekaru saba'in.
Harin dan bindigan na zuwa ne a yayin da ake zaman dar-dar bayan wani samame da sojojin Isra'ilan suka kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Jenin a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Alhamis da ta gabata inda mutane tara suka rasa rayukansu. Isra'ila ta ce, ta kai harin ne da zummar dakile wani gagarumin hari na ta'addanci.