1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan jarida 110 a shekara ta 2015

Gazali Abdou TasawaDecember 29, 2015

Kungiyar kare hakin 'yan jarida ta kasa da kasa ta RSF ta bayyana wadannan alkalumma a cikin rahotonta na shekara-shekara da ta wallafa a wannan Talata.

Symbolbild Journalismus
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Büttner

Kungiyar kare 'yancin aikin jarida ta kasa da kasa ta Reporteurs Sans Frontiere(RSF) ta ce 'yan jarida 110 aka halaka a cikin hanyar gudanar da aikinsu a wannan shekara ta 2015 da ke shirin karewa.

Kungiyar ta RSF ta bayyana wadannan alkalumma ne a cikin rahotonta na shekara-shekara da ta wallafa a wannan Talata.

Kasar Iraki ta kasance a sahun gaban kisan 'yan jaridar a shekarar ta bana da mutuwar 'yan jarida 11 kasar Siriya na bi mata da mutuwar 'yan jarida 10 ,Faransa na a matsayin ta uku da mutuwar 'yan jarida takwas.

Alkalumman na shekarara ta 2015 sun sha gaban na shekara ta 2014 inda aka hallaka 'yan jarida 66 a kan hanyar gudanar da aikin nasu.

A kan haka ne ma Kungiyar ta RSF ta bayyana bukatar ganin ba tare da bata lokaci ba an nada wani wakilin musamman na kare 'yancin 'yan jarida a Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan Jarida 787 ne a cewar kungiyar ta RSF aka hallaka kan hanyar aikinsu daga shekara ta 2005 zoke yau.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW