An kashe 'yan jarida biyu a Iraki
July 7, 2017Talla
'Yan jaridun biyu wadanda ke yi wa gidan talabijan na Huna Salaheddine aiki an kashe su ne a garin Iman Gharbi. Kuma kafar ta ce yanzu haka wani dan jaridar na uku shi ma ya makale a kauyen tare da gawar 'yan jaridar guda biyu sakamakon yadda 'yan tawayen na IS ke ci gaba da yin sintiri a kauyen.