An kashe 'yan sanda a Masar
February 19, 2019Talla
A cewar ma'aikatar tsaron kasar ta Masar, harin wanda aka kai shi da yammacin jiya Litinin ya faru ne a kusa da masallacin nan mai tarihi wato Al-Azhar.
Akwai ma wasu jami'an 'yan sanda biyu da suka jikkata a lamarin.
Wani faifan bidiyo da aka wallafa da safiyar yau Talata, ya nuno 'yan sandan sun taso keyar maharin kafin daga bisani ya tayar da nakiyar da ke a jikinsa.
Da ma dai jami'an na kokarin kama mutumin ne a farautar wasu da ake zargi da kai hari kusa da wani masallacin a birnin Giza a ranar Juma'ar da ta gabata.