1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan sandan Burkina Faso

October 6, 2018

Wasu 'yan sandan kasar Burkina Faso shida sun halaka, a wani harin kwantan bauna da wasu suka kai kan ayarin motocinsu.

Elfenbeinküste Polizei in Bouake
Hoto: Getty Images/AFP

Lamarin da ya auku a garin Solle da ke kan iyakar kasar da Mali, ya faru ne cikin daren da ya gabata, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

Maharan da farko sun buda wuta ne kan ayarin motocin 'yan sandan, kafin su hau kan wasu nakiyoyi da suka daddasa.

Akwai ma wasu 'yan sandan da dama da rahotanni suka ce sun jikkata a lamarin.

Harin ya zo ne kasa da mako guda da wasu maharan suka yi wa wasu sojojin kasar kofar rago, tare da kashe shida daga cikinsu a gabashin Malin.