An kashe yan taliban 11 a Afganistan
August 14, 2006Talla
Dakarun Afganistan sun sanar da kashe mayakan Taliban guda 11,a wata arangama da sukayi a kudancin kasar a yau,ayayinda a hannu guda kuma sojojin kungiyar tsaro ta NATO ,guda hudu ne suka samu raunuka sakamakon tashin wani bomb da motarsu tabi kanta,a birnin Kabul.Kasar ta Afganistan dai na cigaba da fuskantar tashe tashen hankula tun bayan kifar da gwamnatin Taliban da Amurka tayiwa jagoranci a 2001.A gunduwar Helmand dake kudancin kasar ne,yan taliban din 11 suka gamu da ajalinsu,inji mataimakin gwamnan gunduwar Mohammad Akhundzada.Kazalika wani dan kunar bakin wake ya afkawa ayarin motocin dakarun gwamnati da motarsa,inda ya raunanawa 6 daga cikinsu,a gunduwar paktika dake yankin kudu maso gabashin Afganistan din.