1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An katse hanyoyin sadarwa da lantarki a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
October 28, 2023

Da sanyin safiyar wannan rana ce aka tabbatar da katse hanyoyin sadarwa na intanet da wayar salula da ma wutar lantarki a daukacin Zirin Gaza bayan mumuna harin Isra'ila ta kasa.

Gazastreifen I Rauch steigt nach einem israelischen Luftangriff im Gaza-Streifen au
Hoto: Ohad Zwigenberg/AP/picture alliance

A kokari na kakabe mayakan Hamas da Isra'ila ta sha alwashin yi, ta kara tsananta barin wutar a Zirin Gaza. 

Sojojin Isra'ila sun ce sun kutsa maboyar kungiyar Hamas ta karkashin kasa a Gaza, inda rahotanni suka tabbatar da aukuwar gumurzu tsakanin dakarun Isra'ila da na Hamas.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin agaji a yankin sun bayyana damuwarsu a kan rashin sanin halin da jami'ansu ke ciki tun bayan da aka katse hanoyin sadarwa.