1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaNajeriya

Najeriya: Karshen tsadar wankin koda ya zo?

Muhammad Bello LMJ
August 20, 2025

Najeriya ta bayyana rage kudin da asibitocin gwamnatin tarayya ke karba, domin yin wankin koda ga masu fama da larurar cutar koda a kasar.

Najeriya | Gwamnati | Rahusa | Wankin Koda
Ciwon koda, na zaman guda cikin cututtukan da ke kisa a NajeriyaHoto: Jan-Peter Kasper/dpa-Zentralbild/dpa

Da ma dai ba tun yanzu ba, majiyyata da ma 'yan uwan masu cutar ta koda ke kokawa da yadda ake kashe makudan kudi kafin a yi aikin wankin kodar. Gwamnatin ta ce, tuni ta fara wannan rahusa a wasu asibitoci 10 na kasar kafin daga bisani a fadada zuwa sauran asibitocin kasar kafin karshen wannan shekarar ta 2025. A yanzu maimakon biyan Naira dubu 50 a duk lokacin aikin wankin kodar, yanzu Naira dubu 12 kawai za a biya.

Matsalar jini a asibitin Damagaram

03:41

This browser does not support the video element.

Asibitocin tarayya da suka fara aiwatar da sabon tsarin na rahusa, sun hadar da guda biyu a Lagos da daya a Abuja da Owerri da kuma Maiduguri. Sauran su ne na Abeokuta da Azare da Benin, sai kuma na Calabar. Alkaluma dai na nuna cewar, akwai kimanin mutane miliyan 20 a Najeriyar da ke dauke da cutar ta koda. Sai dai kuma wasu bayanai na nuna cewar, dashen koda kyauta ne a wasu kasashen Afrika. Kasashen da ake dashen kodar sun hadar da Sudan da Masar da Afrika ta Kudu, amma fa ga 'yan asalin kasashen kadai.