1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kayyade yan takara takwas a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya

January 19, 2014

Majalissar rikon kwaryar kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta kayyade yan takarar neman shugabancin rikon kwaryar kasar ga mutun takwas.

Zentralafrikanische Republik Übergangsregierung
Hoto: Eric Feferberg/AFP/Getty Images

A wannan Litinin din dai majalissar za ta zabi shugaban da zai gaji Michel Djotodia, da yayi murabus bayan matsin kaimin da ya fuskanta a wani taron kasashen yankin, a kokarin da ake na magance rikicin kasar da yaki ci yaki cinye wa.

Daga cikin yan takarar dai akwai Magajiyar garin birnin Bangui Catherine Samba-Panza, da Désiré Kolingba dan tsofon shugaban kasar André Kolingba, da wani hamshakin dan kasuwa Sylvain Patassé, shima dan tsohon shugaban kasa Ange-Félix Patassé.

Shidai André Kolingba wanda janar ne na soja ya hau karagar mulkin kasar ne a 1981 bayan wani juyin mulki kuma ya jagoranci kasar har ya zuwa shekarar 1993 inda Ange-Félix Patassé ya kada shi a wani zabe da akayi na demokradiya kuma ya rasu ne birnin Faransa a shekara ta 2010, yayin da shi kuma Ange-Félix Patassé ya jagoranci kasar ta Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a karo biyu kafin daga bisani François Bozizé ya tumbuke shi a wani juyin mulki a shekarar 2003 wanda shi ma ya rasu a kasar Kamaru a 2011.

Ana so dai du dan takara ya kasance bashi da wata alaka da yan kungiyar Seleka ta Musulmin kasar, da ma ta anti-Balaka mayakan sa kai mabiya adinin Kirista a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal