1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Barazanar ga zaman lafiyar kasa

Gazali Abdou Tasawa
May 29, 2018

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin fafutikar kare demokradiyya sun koka da yadda bangarorin siyasar kasar ke neman jefa kasar a cikin rudani da tashin hankali a kan batun zabuka masu zuwa.

Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin fafatikar kare demokradiyya na kokawa da yadda bangarorin siyasar kasar ke neman jefa kasar a cikin rudani da tashin hankali a kan batun zabukan da kasar za ta soma shiryawa a shekara ta 2020. Kungiyoyin sun yi hannunka mai sanda ga 'yan siyasar na kowane bangare tare da kira ga su su kai zuciyoyinsu nesa domin samar da fahimtar juna tsakaninsu kafin lokutan zabukan.

Lokacin da ya rage shekaru biyu a gudanar da zabuka a kasar ana ci gaba da samun sabani tsakanin bangaren masu mulki da na 'yan adawa a game da batutuwan da suka shafi tsarin zaben da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar. Wannan lamari ya sanya a kusan kowace rana 'yan siyasar na suka lamiri da kuma zargin juna. Kuma duk kiraye kirayen da aka yi wa 'yan siyasar na su yi hakuri su zauna tebirin sulhu domin shawo kan batutuwan da suke da sabani a kai lamarin ya ci tura inda kowane ya yi tsayiwar gwaman jaki a kan matsayinsa. Lamarin da ya soma tayar da hankalin masu fafutikar kare demokradiyya a aksar ta Nijar.

Hoto: DW/M. Kanta

Da ya ke tsokaci kan yanayin da fagyen siyasar kasar ta Nijar yake ciki a yau, Malam Danbadji Son Allah jagoran wasu kungiyoyin fafatukar kare demokradiyya da hakin dan Adam ya bayyana tsananin bacin ransa dangane da halin da 'yan siyasaar ke neman jefa kasar a ciki kan batun shirya zabukan masu zuwa. Kungiyoyin sun fara wadannan koke-koken ne kwanaki kalilan biyo bayan da jam’iyyun siyasa na kawancen 'yan adawa suka yi fatali da sabon jadawalin zabe suna masu cewar ko kadan hukumar zaben ba ta da yardar jama’a balantana ma ta kai ga yin wani jadawali don tunkarar zabubukan masu zuwa.

Hoto: DW/M. Kanta

Wannan matsalar dai tuni ta sanya kungiyoyin na farar hula masu kare hakin demokradiyya shiga dogon nazari kan dadadiyar tabi’ar ta 'yan siyasar Nijar mai dauke da wanka mai kamar jirwaye. Ba tun yau ba dai ake ta samun takon saka da kai ruwa rana tsakanin bangarorin siyasar kasar musamman ma game da batun shirya zaben 2021 wanda bangaren masu rinjaye ke zargin 'yan adawar da rashin shiri da ma shirya duk wata makarkashiya da za ta kai bangaren masu mulkin ga taka doka ta kundin tsarin mulki, zargin da 'yan adawar ke karyatawa tare da cewar duk wasu abubuwan da ke faruwa a yanzu sale-salin da gwamnatin ta ke son yin amfani da su na ganin ta dauwama a kan madafan iko, kana kafa hukumar ta zabe na kan gaba wajen cimma wannan tsarin.