1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: An koma tebirin sulhu

Gazali Abdou Tasawa
July 4, 2019

A kasar Sudan shugabannin sojin kasar da jagororin masu zanga-zangar neman sauyi sun koma tebirin tattaunawa kan batun kafa gwamnatin rikon kwarya. 

Sudan Treffen zwischen Vertretern des Militärrats und der Demonstranten in Khartum
Hoto: AFP/Getty Images/A. Shazly

Tattaunawar ta yanzu da tawagogin bangarorin biyu ke yi na gudana ne a wani hotel na birnin na Khartoum kusa da gabar kogin Nilu a gaban mai shiga tsakani na kasar Habasha da na kungiyar tarayyar Afirka. 

Bayan da suka share awoyi biyu suna tattaunawa cikin tsanaki a jiya Laraba, inda suka cimma matsaya kan sako dukkan fursinonin siyasa da ake tsare da su, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawar tasu a wanann Alhamis. 

Wannan dai shi ne karo na farko da bangarorin biyu suka sake zama tun bayan da sojojin kasar suka tarwatsa zaman dirshen na masu neman sauyin a gaban harabar hedikwatar sojojin kasar da ke a birnin Khartoum a farkon watan Yunin da ya gabata inda gwamman mutane suka rasa rayikansu.