SiyasaAfirka
Shugaban Senegal ya kori minista kan wasu kalamai
December 31, 2024Talla
Cheikh Oumar Diagne minista mai kula da harkokin mulki a fadar shugaban kasar ya furta kalaman lokacin hira da wata tashar talabijin ta kasar. Tuni aka maye gurbin korarren ministan da Papa Thione Dieng karkashin dokar da shugaban kasar ya fitar.
Karin Bayani: Senegal: Jam'iyya mai mulki na kan hanyar samun nasara
Mai-magana da yawun gwamnatin kasar Moustapha Njekk Sarre ya soki kalaman tsohon ministan da aka kora, inda ya ce sojojin da suka taya Faransa yaki lokacin yake-yaken duniya na farko da na biyu sun kasance wadanda kasar take alfahari da su. Tuni mutane a kasar ta Senegal da ke yankin yammacin Afirka musamman 'ya'ya da jikokin tsaffin sojojin suka fito fili suka yi tir da kalaman ministan da aka kora.