1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kwace wa Senegal nasarar da ta samu a AFCON

March 18, 2026

An kwace nasarar ce saboda 'yan wasan Senegal sun yi fushi kuma sun fice daga filin wasa kafun daga baya su koma.

An kwace wa Senegal nasarar da ta samu a AFCON
An kwace wa Senegal nasarar da ta samu a AFCONHoto: Franck Fife/AFP

An ayyana Maroko a matsayin wacce ta lashe gasar kofin nahiyar Afirka bayan da aka soke nasarar Senegal mai cike da cece-kuce.

Hukumar CAF ta ɗauki wannan mataki na ban ban mamaki ne bayan kwamitin daukaka ƙara ya yanke hukuncin cewa yanzu nasarar ta Maroko ce.

Senegal: Lashe gasar AFCON cikin Labarin Wasanni

Ficewa daga filin wasan, wanda koci Pape Thiaw ya jagoranta, ya jawo tsaiko mai tsawo a wasan.

Bayan da aka sake fara wasan, ɗan wasa Brahim Díaz ya buga fenariti amma mai tsaron raga Edouard Mendy ya tare kwallon.

An kammala wasan kofin Afirka da Maroko ta lashe

A cikin wata sanarwa, CAF ta ce: “Kwamitinta ya yanke hukunci cewa bisa ga sashe na 84 na dokokin kwallon kafar Afirka an ayyana Maroko a matsayin mai nasara.